Yadda Ake Yabon Budurwa

Yau, za mu tattauna ne akan yadda ake yabon budurwa, a fada mata dadadan kalamai masu dauke da dalasiman soyayya wadanda za su sanya ta cikin farinciki da annashuwa.

Masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce, ‘soyayya ruwan zuma ce, a sha, a ba masoyi.’

Babu wanda zai tabbatar maka da gaskiyar abinda na fadi face asalin gurguzun masoyi wanda ke cikin soyayya tsulum-tsulum.

Shi so hana ganin laifi ne. Duk lokacin da kake son budurwa ko kuma take sonka, saboda tsantsar tsagwaron dankon soyayyar nan za ta iya sa budurwar nan taka gaza ganin laifinka, kai ma haka.

Hakan yasa wasu ke yi masa kirari da; so makaho ne!

Yabon Budurwa

Babu wani mutum wanda bai son a yabe shi. Wanda ya fi kowa da komai, kuma ba ya da bukatar komai daga wurin kowa, shi kansa ya umarcemu da mu yaye shi.

Ina ga kuma ‘dan Adam wanda ba komai yake yi duka da zuciya daya ba sai don wannan yabon da yake tsammani daga wurin mutane?

Duk wacce take sonka, ka ke sonta, to, ya kamata ka rinka ware lokaci na musamman yayin da kuke hira, kana yabonta, kana fasa mata kai.

Aradun Allah ba karamin dadi ‘yammata ke ji ba in dai namiji na yabonsu.

Kalmomi za ka na amfani da su wadanda ka ke da yakinin za su yi tasiri a zuciyarta.

Yin hakan akai-akai zai taimaka wurin kara karfin dankon soyayyarka da ke cikin zuciyarta.

Ka guji yawan kushe budurwar da kuke tare da ita, domin ba ita ba, kai ma ba ka so a rinka kallon cikin idanunka ana kushe ka ba.

Ko da kuwa kushewar ta raha ce.

In har ba ta nuna rashin jin dadinta a zahiri ba, can cikin karkashin zuciyarta hakan zai yi mata ciwo kwarai da gaske.

Wadansu Kalaman Yabon Budurwa

Bai kamata na yanke igiyar rubutun nan nawa ba ba tare da na zayyano muku wadansu kalmomi wadanda ake amfani da su wurin yabon budurwa ba.

Har cikin raina, na san in na yi muku haka to ban kyauta ba, kuma na ci amanar soyayya ko da kuwa bana yinta yanzu haka.

Su wadannan kalmomi su ne;

  • Haba abar kauna, a duk fadin duniya bana tunanin akwai wacce ta kaiki matsayi cikin zuciyata.
  • Kina da kyakkyawar sura masoyiya. In na ce sura, ina nufin sura, sura irin wacce ake bugawa a jarida.
  • Duk lokacin da na kasance tare da ke kina saka ni farinciki, jin dadi da nishadi. Hakika ke din nan ta daban ce.
  • Magana ta gaskiya habibiyata, duk inda ake neman mace wacce ta cika kuma ta amsa sunan mace, to, lallai kin kai. Wayyo! Ina ma Allah ya mallaka min ke…
  • Murmushinki tamkar na zinare haka yake, dariyarsa mai dauke da kyakkyewa mai dadin ji. Lallai na yi dace!
  • Ko a cikin mata, kin ciri tuta, irin tutar da sai an kidanya metan dubu kafin a samu kamarki. Gaskiya ke din ta daban ce.

Kammalawa

Irin wadannan kalaman wadanda ke dauke da tarin yabo su ya kamata lokaci zuwa lokaci ka rinka jefawa a cikin zancenka da budurwarka.

Kada ka ji kunyar komai, a yi komai ba koma, duk a cikin love ne.

Your reliable editorial desk, which publishes well-crafted articles just for you at Avitro. We are really good at what we do!

Related Posts