Yadda Naci Sirikata

Lalle marhaban da zuwa shi wagga shafi, ni Mudi Ɗan Indo mai gudanawarwa yau zan baƙu wani labari.

Labarin dai bai faru da gasken-gaske ba, ƙirƙirarre ne, don haka na bayar da shi ne saboda kawai ku nishaɗantu

Amma kafin na fara, yana da kyau in tuna muku cewa zina babu kyau, mai yin ta taɓaɓɓe ne, ballantana luɗi wadda shi duk wanda ya ke yinsa taɓewarsa ta fi ta kowanne taɓaɓɓe.

Gabatarwa

Sunana Mudi Ɗan Indo, daga ƙauyenmu na Sogiji na tattara kayana ciff na tafi ci-rani Abuja.

Abinka da wanda bai da wanda ya sani a can, ga birni ba ƙauyenku ba, inda za ka rakaɓe ka kwana ma babbar ja’iba ce.

Amma da ya ke bariki cike take da kowaɗanne irin mutane, kwanaki huɗu da dirata, ranar farko a kwantaina na kwana bisa kwali ni da wasu Katsinawa.

Kashegari ma haka, bayan na ɗan yi kwanaki a birnin ga, na ɗan sassan wurare, sa’anna sana’ar da nake yi dako ce.

Rannan sai Allah ya haɗa ni da wani mutum, wanda jininmu ya haɗu da nasa. Kai da ganinsa ka san shi ma ɗan ciranin ne, amma fa yanayinsa ya nuna ba a cikin wahala ya ke ba.

Lokaci ya lula, kwanaki suka shuɗe, har ta kai ga cewa na ƙara shaƙuwa da abokin nan nawa mai suna Litiyo.

Na kuma lura kamar shi fa sam bai sana’a ko aiki komai, kurum zaman kashe wando yake yi. Na kuma kalli kaina, na ga da dakon ma da yaya nake iya ciyar da kaina a barikin nan na yi tul-tul bare kuma ba na yin koma?

Jikina ya bani, lallai akwai wata hanyar da Litiyo ke bi wurin samun kuɗi saboda haka nan take na sha alwashin sai na tambayeshi takamaimai aikin me yake yi.

Isa ta Abuja

Bayan kwana biyu, rannan muna zaune ni da shi, sai alwashin nan nawa ya faɗo min, me kuwa zan yi in ba tambayarsa ba?

Sai na ce, “Litiyo, na ga ba ka kataɓus a birnin nan, ga shi kana mutsitstsikar duniyarka yadda ka ke so. Wai shin maye sirrin ne?”

Litiyo ya yi shiru kamar yana nazari, can sai ya daɗo kai ya kalleni ido cikin ido sannan ya fara da cewa, “Mudi, ban so ka yi mini wannan tambayar ba, amma dalilin ƴar abotar nan tamu zan baka amsa!”

Ya nisa sannan ya cigaba da cewa, “Ba na sana’ar komai sai jin daɗi kuma a biya ni.”

Na kalleshi irin na ji abu ya yi min bambaraƙwai din nan, na ce, “Ban fahimceka ba, yi min ƙarin haske.”

Ya ci gaba, “Ai ni nan da ka ganni, kullum da daddare a gidan alfarma na ke kwana.”

Cikin azama na tari numfashinsa kafin ya cigaba na ce, “Kam bala’i, ta yaya za ka kwana a gidan alfarma bayan kai ma ɗan cirani ne kamata? Ina dai a kwantaina ka ke kwana? Ban da ƙarya please!”

Ya yi ƴar dariya sannan ya ce, “Har yanzu ka gaza ɓaro jirgin, to dallah malami ina kwana a gidajen alfarma ne saboda Hajiyoyi na ke wa sabis.”

Nan na tuntsire da dariya na ce, “Ka ji maƙaryaci, wai Hajiyoyi ka ke wa sabis, aka ce maka su ɗin mota ce?”

Ya ɓata rai ya ce, “Shi kenan, tun da ka ƙaryata ni, yau bayan Sallar Isha ka biyo ni domin gane wa idonka abinda nake yi.”

Nace, “Allah ya kaimu, za mu ga ta yadda za ka kwana a gidan alfarma kana Ayuhannasi.”

Daga nan sai muka sauya akalar hirar ta mu, har zu wani lokaci kafin mu rabu akan in dare ya yi za a nuna min abinda ake samun ƙudi a kuma ji daɗi.

Daren Farko

Dare na ɗan rakawa sai na aza takalma bisa ƙafata, sannan na nufi inda mu ka yi da Litiyo za mu haɗu.

Ko da naje sai na iske bai ƙaraso ba, saboda haka sai na samu wuri na faka ina jiran isowarsa.

Jimawa kaɗan sai ga Litiyo ya ƙaraso, nan na miƙe muka gaisa sannan ya shige gaba ina binsa a baya har zuwa wani junction wanda ke cike da lafiyayyun samari a tsaitsaye a gefen titi.

A zuciyata nace waɗannan ko uwarsu suke yi a tsaitsaye haka? Oho dai.

Muna isa sai Litiyo ya koma gefe shi ma ya ja tunga, ya min nuni da nima na ja tunga a gefensa.

Ba musu na yi hakan.

Motar Sirikata

Ba a ɗauki wani dogon lokaci ba sai ga wata luntsumemiyar mota ta zo ta faka a gefenmu, na ga samarin nan suna matsowa kusa da ita.

Abinka da wanda bai san kan gari ba, sai na maze na cigaba da tsaiwata a wurin da nake.

Jimawa kaɗan sai aka sauke gilashin motar. Wata kyakkyawar mace na hango cikin motar wadda ba za ta wuce irin 39 years ɗin nan ba. Wayyo Allah na! Lallai in da mata suke suna can, in da mata-mata suke su ma suna can (wato ruwan kashe gobara).

Hajiyar nan ta matukar tafiya da ni, gaskiya ba adawa Allah ya hore mata kyau babu adawa.

Gani na yi matasa suna zuwa suna kewaya motar nan kamar ƙudaje sun ga sabon kashi. Ashe in har mota ta faka, to matasa ne ke zuwa suna yin layi, sai mace ta zaɓi wanda ya yi mata ta tafi da shi gida domin ya biya mata buƙatarta.

Mutane fiye da goma ne Hajiyar nan ta kalla, amma ga dukkan alamu ba ta ga wanda ya yi mata ba, hakan ya sa babu wanda ta yi wa izinin ya shiga motar ta.

Da dai na ga abin na yi ne, sai na yanke shawarar matsawa kusa domin na samu damar ƙare wa Hajiyar nan kallo sosai.

Ko da na matsa kusa, ina cikin kallonta sai na ji kamar daga cikin wata ƴar siririyar daɗɗaɗar murya an ce, “Kai ɗan Samari mai rigar Polo.”

Na yi wuri-wuri, na kalli haggu, na kalli dama na amma ban ga wanda ta ke yi wa magana ba, sai abokina Litiyo ya taɓa kafaɗata ya ce, “Mudi da kai fa ta ke.”

Na yi firgigit na ce, “To, bari na matsa kusa.”

Nan ma matsa bakin motar, muka gaisa da Hajiyar nan. Kai wallahi muryarta da ɗan shegiyar daɗi take.

Bayan mun ɗan yi musayar yawu, sai ta ce min na shigo mota.

To, ni dai har zuwa lokacin kaina a cikin duhu yake, amma dai na yi ta maza na kunna kaina cikin motar nan ta Hajiya.

Abokina Litiyo da sauran samarin da ke tsaitsaye a wurin su ka ɗan ɗago mini hannu ɗauke da wani irin murmushi a fuskarsu. Ga dukkan alamu na yaƙe ne. To, amma ni ina ruwana? Babu.

Abin da dai na faɗa a zuciyata shi ne: muje zuwa.

Kammalawa

A nan fa za mu dakata, sai wani jikon. In har marubucin labarin nan ya ci gaba, to, za ku ga mun kwafo shi mun kawo muku shi.

Your reliable editorial desk, which publishes well-crafted articles just for you at Avitro. We are really good at what we do!

Related Posts