Sahihan Hanyoyin Hana Daukar Ciki Guda Shida

Yau, da yardar Allah za mu yi cikakken bayani a kan hanyoyin da ake bi wurin hana daukar ciki.

Bin wadannan hanyoyi ba wai an kadaita su ba ne kawai ga maza, la la, hatta mata ma akwai hanyoyin da za su bi wurin hana daukar ciki walau kafin tarawa ko kuma bayan tarawa.

Kafin na yi nisa cikin wannan jawabi, zan so sanar da ku cewa; ni fa ban kasance likita ba, kawai dai bincike zan yi game da wannan matsala domin na sanar muku da abinda yake available.

Daukar Ciki

Gagarumin abu ne a wurin wadansu mutanen, musamman in har mutum matarsa ce yake sa ran ta dau ciki domin ta haifa masa magaji ko kuma magajiya.

Amma, ga sashen mazinata, ko kusa, ko alama, ba sa kaunar su kwanta da mace har ta kai ga daukar ciki domin wadansu daga cikinsu wadanda ba su ci kai ba, gani suke in har suka yi cikin shege to fa sun yi abin kunya.

Wasu lokutan a kan samu matsala wurin samun ciki, mutum ya yi ta fama, amma abu ya ci tura.

Haka kuma, wasu na yanke hukunci ne gaba-gadi yayin da aka samu matsala irin wannan, amma in son samu ne, a je ga likita ya yi bincike a ilimance domin gano bakin zaren.

Hanyoyin Hana Daukar Ciki ga Mata

Ba kowacce mace ce za ta yi amfani da daya daga cikin wadannan hanyoyi da za mu yi bayaninsu a kasa ba da zummar aikata fajirci.

Bisa wannan dalili, shi yasa za mu yi warwara yanzu haka.

1). Kwaroron Roba

Yin amfani da kwaroron roba (kwandam) na daya daga cikin fitattu kuma shahararrun hanyoyin hana daukar ciki.

Shi kansa kwaroron robar iri-iri ne, akwai na maza, akwai kuma na mata.

In har ke macece, wacce ke son dakile shigar ciki bayan kammala saduwa da mijinki ko kwartonki, to kawai ki yi amfani da kwaroron roba wanda yake na maza.

Kamar bayanai suka tabbatar, shi irin wannan kwaroron robar a cikin farji ake saka shi kafin fara saduwa.

Kuma bayan hana daukar ciki ma, yana taimakawa wurin kare mace daga daukar cuttukan da ake dauka sakamakon jima’i, kamar su sanyi, cuta mai karya garkuwar jiki da sauransu.

Sannan, magana ta gaskiya, shi kwaroron roba ko ma wanne iri ne, yana rage dadin jima’i.

2). Kwaya (capsules)

Akwai kwayoyin da likitoci ko kuma masu kyamis suke bayarwa wacce take hana daukar ciki.

Kuma su ana amfani da su ne bayan an kammala saduwa bai wuce da ‘yan mintuna ba, ko awa daya.

Da zarar kun kammala saduwa, sai ki dauki kwayarki ki afa, sannan ki bi ta da ruwa.

Ba zan iya fada muku sunanta ba, amma dai ku tuntubi likita domin shi ne wanda ya san wacce kwaya ya kamata ya baku.

A wata jita-jita da na ji, wai ita wannan kwayar ta hana daukar ciki in aka cika shanta, to tana jawo rashin haihuwa, domin lalata mahaifa ta ke yi.

Ban fa tabbatar ba, amma ku tambayi likita, zai fada muku gaskiya.

3). Allura

Allura dai kala-kala ce, akwai ta zazzabi akwai da hana daukar ciki, daidai matsalarsa, daidai shan allurarka.

Akwai allurar da ake yi a asibiti ga mata wacce take taimakawa wurin hana daukar ciki.

Ita wannan allura, ana yinta ne na wani ‘dan takin lokaci (kamar watanni biyu, uku, dss).

Amma fa in da son samu ne, mace ta rinka zuwa akai-akai asibiti ana mata sabuwa domin tabbatar da dakar da shigar ciki na tsawon shekara daya ko biyu ga ma’auratan da ke son bayar da ratar haihuwa tsakanin ‘ya‘yansu.

In kuma ke mai aure ce, to, za ki iya yin allurarki, kuma kuci gaba da tarawa da maigidanki ba tare da yin amfani da kwaroron roba ba ko wani abu makamancin haka.

Domin neman karin cikakken bayani akan allurar hana daukar ciki sai ku tuntubi likitanku.

4). Guru

Akwai masu maganin da ke baiwa mata guru wanda ke taimakawa wurin hana daukar ciki.

Na tabbata wadansu za su ce ai daura guru shirka ce, to, ko mai dai menene ni babu ruwana.

Ga wacce ke son dakatar da shigar ciki cikin sauki, sai ta nemi wani shahararren mai maganin ya hada mata gurun hana daukar ciki.

Bayan ya bata, sai ta wuce wurin baduku ya rufa mata shi amma ba da fata ba don ba ta lasting, a rufa shi da tsumma, sai ta daura.

5). Hoda

Rahotanni sun tabbatar da cewa, akwai wata hoda yanzu haka da ake siyarwa a shagunan magungunan musulunci wacce take taimakawa wurin hana daukar ciki.

Ita wannan hoda, ance mata ne ke shafata a gabansu, gabanin saduwa.

Kamar yadda wadanda suka jarrabata suka tabbatar, sun ce kwarai da gaske tana hana daukar ciki ko da kuwa namiji ya kawo a farjin mace.

Amma fa, a likitance, babu wani labari wanda ya tabbatar da sahihancin hodar.

Haka kuma hukumar kuda da tace magungunan da abinci ta NafDac, ba ta tantanceta ba.

6). Rubutu

Akwai malaman zaure wadanda suke yin rubutun da ke hana daukar ciki kwata-kwata.

In aka yi miki shi, to, ba za ki dau ciki ba har sai lokacin da kike so.

A hakan ma, in kina son daukar cikin, to, dole sai kin je wurin malamin nan ya kara miki rubutu wanda zai karya wancan lakanin hana daukar cikin.

Wannan hanyar sahihiya ce, kuma an tabbatar da cewa tana da matukar tasiri wurin hana daukar ciki ga karuwai da masu aure.

Kammalawa

Hakika shi ilimi kogi ne mai matukar zurfin da duk iya iya iyon mutum ba zai kure shi ba.

Za ta iya yiwuwa a cikin rubutun nan nawa akwai abinda na manta ban zayyano ba, ko ma kwata-kwata ban san da shi ba wanda kuma shi ma yana hana daukar cikin.

Kada ku ji babu dadi don na gaza ta nan bangaren, domin iya abinda na bincika shi na kawo muku.

In har kuna da wasu shawarwari da za ku bayar, ko kuma gyare-gyare a cikin wannan rubutu nawa, to, sai ku yi mana magana ta adireshin imel dinmu.

Your reliable editorial desk, which publishes well-crafted articles just for you at Avitro. We are really good at what we do!

Related Posts