Hanyoyin Samar da Arziki Guda Biyar (5) Sahihai

Kamar yadda komai ke da lokacinsa, to, haka shi ma arziki yake da nasa lokacin. Duk halin tsiya da matsi da mutum ke ciki in dai lokacin yin arzikinsa ya yi, to babu tantama sai ya yi.

Akwai hanyoyi masu tarin yawa wadanda ake bi domin ayi arziki, ba kuma lallai su lissafu ba.

Zabi na ga wanda ke son ya yi arzikin ko kuma ya nemi arzikin, sannan yana da kyau mu yi sani cewa shi arziki abu ne wanda sai lokacinsa ya yi ake yinsa.

Ina da yakinin wadansu mutanen a matukar matse suke su ga sun yi bankwana da talauci, sun fi karfin bukatunsu har ma da na ‘yan‘uwa.

Kai tsaye ba tare da bata lokaci ba, zan bayyano wadansu nau’ikan hanyoyin neman arziki hadi da yin bayani a kansu.

Hanyoyin Neman Arziki

  1. Kasuwanci
  2. Sana’ar Noma
  3. Sana’ar Kiwo
  4. Siyasa
  5. Kasuwar Yanar Gizo

Kasuwanci

Kasuwanci na daya daga cikin mashahuran hanyoyin da ake bi wurin neman arziki kuma a yi kudi nan-da-nan da yardar Allah.

In dai muradinka a rayuwa shine ka yi kudi, to a shawarce kawai ka nemi wata sana’a wacce ka san lallai tsurar kudi ake zubawa a cikinta a nemi kudi ka farata.

In kuma baka da jarin farawa, sai ka ciwo bashi ko kaje ka yi aikin karfi ka tara kudinka domin fara kasuwanci.

A shawarce kada ka raina kasuwa ko yaya take, domin da zarar Allah ya sa albarka cikin lamarin wannan kasuwa taka nan da nan sai ka ga ka zama abin sha’awa a garinku, jiharku kai harma da kasa baki daya.

Nau’ikan kasuwancin da ke kawo kudi

  1. Siyar da mai (fetur, gas da cooking gas)
  2. Kasuwar atamfofi da sutura
  3. Siyar da kayan masarufi
  4. Siyar da mai (man gyada, kwanti, manja da sauransu)
  5. Siyar da kayan lantarki (wayoyi, kwamfiyutoci da kayayyakinsu)
  6. Siyar da kayan gini (bulo, siminti, kusa, katako)
  7. Siyar da kayan kawar gida (carpets, fenti, rugs, katifu, kujeru da sauransu)
  8. Siyar da kayan makulashe da kayan sanyi
  9. Siyar da abinci da sauransu.

Hakika akwai tarin nau’ikan kasuwanci wadanda in dai akwai kudin da za ka je ka yiwo sari ka sayar, to ka zabi wacce kake gani ta kwanta maka a rai ka fara.

Sana’ar Noma

Noma dai kusan kowa ya san shi, in ma bai sanshi a aikace ba, to a zahirin gaskiya ya sanshi a sunance.

Babu wata sana’a wacce ke baiwa mai karfi da marar karfi damar cin albarkacin kasa da ruwa fiye da sana’ar noma.

Ga kirarin noma; “Na duke tsohon ciniki, kowa ya zo nan duniya kai ya taras.”

Kididdigar masu kididdiga ba za ta iya bada ainihin tarin al’ummar da suka samu sauyin rayuwa a tsakanin shekaru 8 zuwa 9 da suka shude ba sakamakon sauye-sauye da aka samu a bangaren na noma.

Gwamnatin tarayya ta matukar taimakawa manoma ta hanyar dakile shigo da wadansu nau’ikan abinci kamar su shinkafa, taliya da sauransu domin farfado da harkar noma a kasarmu ta Najeriya.

Shi yasa a shawarce in dai mutum yana da kudi, kuma yana da sha’awar yin noma a matsayin sana’a, to gaskiya ya nemi masana a harkar domin su shige masa gaba ya nemi arziki.

Ko-da-nace masana abin, ba fa ina nufin farfesoshi da manyan malamai ba, a’a, ya nemi ainihin manoma talakawa domin sun san kan sabgar sosai.

Ko goron wuri zai karba, in suka leka suka fahimci wurin bashi da inganci, in ya noma zai yi hasara, to lallai za su fada masa gaskiya.

Game da kula da lafiyar tsironsa, wannan sai ya samu kwararru wadanda sana’arsu kenan noma, ya rinka mu’amala da su, yana kuma neman shawara a garesu.

Rabe-raben Noma

Noma ya karkasu gida-gida.

Kada ka yi tunanin kawai noman shinkafa shi kadai ne noma, a’a, wasu fa ridi suke noma, wasu zobo, wasu barkono, amma an fi raja’a akan shinkafar.

Ga jerin nau’ikan noma nan;

  1. Noman hatsi (gero, dawa, masara, maiwa, farfara)
  2. Noman shinkafa (yar Thailand, jeep, jamila da sauransu)
  3. Noman alkama
  4. Noman wake
  5. Noman gyada
  6. Noman zobo
  7. Noman doya
  8. Noman rake
  9. Noman auduga
  10. Noman tumatir
  11. Noman kayan marmari (lemo, kankana, cucumber, ayaba, gwanda, kwakwa da sauransu)
  12. Noman ridi
  13. Noman aya
  14. Noman tattasai
  15. Noman attaruhu
  16. Noman kayan ganye (salad, kabeji da sauransu)

Magana ta gaskiya, ba zan iya kawo dukkanin nau’ikan noma ba, sakamakon kasarmu fadi gareta.

Abinda muke nomawa a nan ba lallai shi kuke noma a naku wurin ba.

Kai dai ka zabi wanda ka fahimci kasuwarsa tana matukar ci.

Abinda kasuwarsa take kan gaba wurin kawo kudi shi ne noman shinkafa da sauran kayan abinci.

Saboda haka ku zabi wanda kuke ganin ya fi muku.

Sana’ar Kiwo

Duk wanda kaji yana maganar sana’ar kiwo ba ta kawo kudi, ko kuma ba a yin arziki da ita, to kawai ka fada masa cewa ya jahilci sana’ar kiwo cike da wajenta.

Bayan sana’ar noma babu wata gangariyar hanyar samar da arziki in ka dauke kasuwanci fiye da kiwo.

Na tabbata wadansu daga cikinku za su yi mamaki kan jin na lissafto wannan mashahuriyar sana’a ta kiwo a matsayin hanyar samun arziki.

To, amma bari ku ji;

Sana’ar kiwo ba wai tana nufin lallai sai mutum ya makala sanda ya kora shanu da tumaki yana zagawa da su dazuka suna cin ciyawa ba.

Rabe-raben Sana’ar Kiwo

  1. Kiwon shanu
  2. Kiwon tsuntsaye (kaji, agwagi, tala-talo da sauransu)
  3. Kiwon awaki
  4. Kiwon tumaki
  5. Kiwon kifi

Wanne Irin Kiwo Ya Fi Kawo Kudi

Kiwon tsuntsaye na daya daga cikin fitattun hanyoyin kawo kudi a sana’ar kiwo, in karya nake yi ku tambayi masu gudanar da gidajen gona za su baku labari.

Na farko za ku sayar da kwayayensu, ku kuma sayar da kajin kansu.

Sannan kiwon kifi ma babbar sana’a ce, in kun musa ku tambayi kwarawa za su fada muku gaskiyar lamari.

In professionally kake son yin harkar kiwon kifi to sai ka hada masa lake ka tanadi abinci, ke nemi irin kifi, ka kuma tanar masa mai kula da shi.

Kiwon shanu da tumakai da awakai ma ba a barshi a baya ba wurin kawo manya-manyan kudade.

Shi yasa, za ku ga mutum ya sayi shanu kamar hamsin ya bayar kiwo, cikin shekaru biyu sai ka ga sun zama 80.

Babu abin rainawa a sabgar sana’ar kiwo ko ma wanne irin kiwo za ku yi. Ku dai ku bidi sa’a.

Siyasa

Sanin kanku ne yanzu an maida siyasa kamar wanin high-class business, kowa shiga yake domin ya zuba ya kwashe.

Hakane ma ya sa na lissafo kasuwar siyasa a matsayin mashahuriyar hanyar samar da arziki mai maiko.

In dai kudi kake son yi dare daya, to kawai ka shiga siyasa, ka zuba kudi ka ci zabe, ka kwashe abinda ka zuba.

Kada ku ji haushina domin na maida siyasa a matsayin sana’a.

A’a.

Ya kamata mu kalli abin a hankalce, mu kuma yi masa duba na tsanaki na gaskiya.

In dai arziki kake son yi na ko ma yaya ne, to kawai ka zama ‘dan siyasa.

Kasuwar Yanar Gizo

Kasuwanci a yanar gizo tamkar kasuwanci ne na zahiri, bambancinsa daya ne da kasuwancin zahiri.

Shi ko wannan bambanci ba wani abu ba ne face; ga kudi ga kaya da kuma ga kudi, kaya zai iso daga bay

Kasuwanci ta yanar gizo ya ginu ne ta hanyar tsantsar yarda tsakanin mai saye da mai sayarwa

Rabe-raben Kasuwancin Yanar Gizo

  1. Sayar da kayayyaki
  2. Sayar da kayan waya ko wayoyi
  3. Sayar da nau’ra mai kwakwalwa
  4. Sayar da turame, huluna, takalma da sauransu.
  5. Yin kwadago

Gaskiya ba zan iya jero baki dayan irin kasuwancin da ake yi a yanar gizo ba, amma dai suna da yawa kam.

Your reliable editorial desk, which publishes well-crafted articles just for you at Avitro. We are really good at what we do!

Related Posts